(ABNA24.com) Matakin na gwmanatin kasar India ya biyo bayan mako guda na tashe-tashen hankulan da yankin na Kashmir ya fuskanta. Gwamnatin kasar ta India, ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta yi kira ga dukkanin masu zuwa yawon bude ido yankin da su daina saboda tabarbarewar harkokin tsaro.
Kasashen India da Pakistan sun zargi juna da haddasa rikici a cikin yakin na Kashmir a cikin makwannin bayan nan. Gwmanatin India ta zargi Pakistan da tunzura wasu kungiyoyin da suke a yankin na Kashmir kamar “Jaish Muhammad” wajen tayar da hankali.
Ita kuma Pakistan ta zargi India da cewa ta yi amfani da bama-bamai da aka haramta akan fararen hula a yankin.
Kasashen biyu dai sun yi yaki da juna a lokuta da dama akan yankin na Kashmir.
/129
Matakin na gwmanatin kasar India ya biyo bayan mako guda na tashe-tashen hankulan da yankin na Kashmir ya fuskanta. Gwamnatin kasar ta India, ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta yi kira ga dukkanin masu zuwa yawon bude ido yankin da su daina saboda tabarbarewar harkokin tsaro.